✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe matashi a rikicin teburin mai shayi

Wata takaddama da ta kaure tsakanin wasu matasa a teburin mai shayi ta yi sanadiyyar kashe daya daga cikinsu mai suna Umar Abubakar a unguwar…

Wata takaddama da ta kaure tsakanin wasu matasa a teburin mai shayi ta yi sanadiyyar kashe daya daga cikinsu mai suna Umar Abubakar a unguwar Aisami ta Karamar Hukumar Gwale a cikin birnin Kano.

Umar ya gamu da ajalinsa ne bayan da wani matashi wanda yanzu haka ya ke komar ’yan sanda ya daba masa wuka.

Kakakin Rundunar ’Yan sanda ta jihar Kano DSP Abdullahi Haruna Kiyawa ya tabbatar da faruwar lamarin.

Ya ce Umar ya riga mu gidan gaskiya ne jim kadan bayan jami’ansu sun garzaya da shi Asibitin Kwararru na Murtala Muhammad da ke Kano.

Kiyawa ya ce tuni dai Kwamishinan ’Yan Sandan Jihar, CP Habu Sani ya ba da umarnin fadada bincike kan batun tare da gurfanar da wanda ake zargin gaban kuliya don ya girbi abin da ya shirya.