✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 11 a sabon hari a Katsina

An binne gawar mutum 11 ana kuma ci gaba da neman wadanda ba a gani ba.

Akalla mutum 11 ne daga kauyen Dan-Kumeji a Karamar Hukumar Kankara ta Jihar Katsina suka rasa rayukansu a wani sabon hari da ’yan bindiga suka kai.

Aminiya ta kuma gano mutum shida da suka ji rauni na asibiti, inda ake ba su kulawa.

Wani mazaunin kauyen mai suna Abdulmumini Sani, ya tabbatar wa Aminiya faruwar lamarin ta wayar tarho, inda ya ce maharan sun kai wa kauyen farmaki ne da misalin karfe 11:30 na daren ranar Alhamis.

“Lokacin da mutanenmu suka hange su sai kowa ya fara gudu, ba tare da sanin cewa maharan sun karkasu ba. Kai tsaya suka shiga harbin wadanda suka fara gudu,” a cewarsa.

Ya kara da cewa da safiyar ranar Juma’a an gano gawar mutum 11, kuma an yi musu sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanadar, sannan an ci gaba da neman gawar ragowar mutanen da ba a gani ba.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, mun yi kokarin jin ta bakin kakakin ’yan sandan Jihar Katsina, SP Gambo Isah, amma hakarmu ba ta cim-ma ruwa ba.