✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 112, an sace 160 a Kaduna da Filato a wata daya – Rahoto

Rahoton ya zargi hukumomin Najeriya da gazawa wajen kare ’yan kasa

Wani rahoton kungiyar kare hakkin bil-Adama ta Amnesty International ranar Litinin ya ce akalla mutum 112 ne aka kashe, wasu 160 kuma aka sace su a cikin wata daya a Jihohin Kaduna da Filato.

Rahoton, wanda ya yi nazari tsakanin watannin Yuli zuwa biyar ga watan Agustan 2021 ya kuma zargi hukumomin Najeriya da gazawa wajen sauke nauyin kare ’yan kasa.

Rahoton ya ce, “Bincikenmu ya nuna cewa duk da cewa akwai alamun barazanar samun harin ramuwar gayya a wasu wuraren, ba a yi wani katabus ba wajen kare jama’a. Lamarin da ya sa rikicin ya ci gaba da kazancewa.

“Ban da yin Allah-wadai da fitar da sanarwa in an kai hari, ya zama wajibi gwamnatoci su tashi tsaye su hukunta masu tayar da zaune tsaye,” inji Osai Ojigho, Daraktar kungiyar a Najeriya.

Ta ce bincikensu ya kuma gano cewa akalla mutum 78 ne aka kashe, wasu 160 kuma ’yan bindiga suka sace tsakanin uku ga watan Yuli zuwa biyar ga watan Agustan 2021 a Jihar Kaduna, ciki har da daliban makarantar sakandiren Bethel da ke Jihar.

“A Jihar Filato kuma, an kashe mutum 34, ciki har da wasu makiyaya mutum bakwai wadanda aka kai wa hari ranar daya ga watan Yuli a kauyen Dogon Gaba, da wasu biyu kuma da aka kashe a kauyen Fusa lokacin da suke kokarin nemo shanunsu da suka bace.

“Manoma da ke kauyukan da abin ya shafa sun shaida wa Amnesty International cewa ana kai wa mutanen da ba su ji ba, ba su gani ba harin ramuwar gayya.

“Irin jan kafar da hukumomi ke yi na taka muhimmiyar rawa wajen kara ta’azzarar hare-haren.

“Ya zama wajibi hukumomin Najeriya su tashi tsaye su magance lamarin. Tsawon wanne lokaci za a ci gaba da zama kafin a lalubo bakin zaren?,” inji Daraktar.