✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kashe mutum 285, an sace 1,789 a wata 6 a Kaduna —Rahoto

An kashe mutum 285 a Jihar Kaduna cikin wata shida sakamakon rashin tsaro

Jami’an tsaro sun hallaka ’yan bindiga 161 a cikin wata shida a Jihar Kaduna.

Gwamnatin jihar, ta ce a cikin wata shidan da suka gabata, ’yan bindiga sun yi garkuwa da akalla mutum 1,789 a sassan jihar.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce jami’an tsaron sun kashe ’yan bindiga 59 a tsakanin watan Afrilu zuwa Yulin 2022.

Rahoton yanayin tsaron jihar na wata shida da ya gabatar ranar Juma’a ya ce an kashe mutum 285 a sassan jihar, sakamakon ayyukan ’yan bindiga da rikicin kabilanci da sauransu.

Ya ce daga watan Yuli zuwa Satumba kuma an yi garkuwa da mutum 804 a jihar, wadanda 508 daga cikinsu an sace su ne a yankin Mazabar Kaduna ta Tsakiya.

Ya ce a jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 109 a musayar wuta daga watan Yuli zuwa Satumba.

Kwamishinan tsaron ya ce a cikin wata ukun, an sace shanu 1,133, kuma mutum 654 da ake zargi sun shiga hannu.