✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Yadda aka kashe ’yan bindiga 69 a Kaduna

’Yan bindiga sun sace mutum 830 da dabbobi 1,018 a wata uku a jihar Kaduna.

Jami’an tsaro sun kashe ’yan bindiga 69 a dauki ba dadin da aka yi tsakaninsu a Jihar Kaduna a cikin wata ukun da suka gabata.

Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Jihar Kaduna, Samuel Aruwan, ya ce an kashe ’yan bindiga da dama a hare-haren da jiragen yaki suka kai kan maboyarsu a sassan jihar.

Aruwan, wanda ya sanar da hakan a ranar Laraba ya kara da cewa ’yan bindiga sun sace mutum 830 da dabbobi 1,018 a jihar.

Da yake gabatar da rahoton tsaron jihar na watan Yuli zuwa watan Satumban 2021, Aruwan ya ce daga cikin mutum 830 da aka yi garkuwa da su, mutum 732 da dabbobi 780 an  sace su ne a Mazabar Kaduna ta Tsakiya, wadda ta kunshi kananan hukumomin Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Kajuru da Chikun.

Bugu da kari, an jikkata mutum 210 a hare-hare daban-daban da aka kai, ciki har da na ramuwar gayya a rikicin kabilanci.

Ya ce an samu rahotanni 77 game da lalata amfanin gona a jihar, musamman a yankunan Birnin Gwari, Giwa, Igabi, Chikun, Kachia, Kauru, da Zangon Kataf.