An kashe ’yan Boko Haram 9 ta hanyar harbi da kibiya a Borno | Aminiya

An kashe ’yan Boko Haram 9 ta hanyar harbi da kibiya a Borno

    Sani Saleh Chinade

’Yan kabilar Kwayam da ke Gabashin jihar Borno sun kashe ’yan ta’addan Boko Haram su tara ta hanyar harbi da kibiya a wata arangama a ranar Laraba. 

Wata majiya mai tushe ta shaida wa Zagazola Makama, wani mai sharhi kan harkokin tsaro kuma masani kan yaki da ta’addanci a tafkin Chadi, cewa an kawar da ’yan ta’addan ne a wani harin ramuwar gayya da suka kai a kauyen Kakari da ke karamar hukumar Guzamala a jihar Borno.

Majiyar ta kuma ce mutanen yankin sun kashe wasu ’yan ta’adda biyu da suka kai hari a kauyen Kuda a wani yunkuri na satar shanunsu da bai yi nasara ba a ranar Talata.

Ya ce a ranar Larabar, ’yan ta’addan sun tattara mayakansu a kan babura bakwai a wani yunkurin da suka yi domin daukar fansa kan kisan mutanensu biyu.

Ya ce da isowarsu, mutanen yankin da suka shahara da dabarun yaki na gargajiya, sun nakasa bindigar AK-47, kafin su kashe su ta hanyar amfani da kwari da kibiya mai guba.

’Yan ta’addan da kibiyoyi suka harba sun mutu a cikin kasa da mintuna 10 yayin da sauran suka sha da kyar.

Kwayam dai na daya daga cikin manyan kabilu a jihar Borno daga bangaren kabilar Kanuri.

Ana samun su a yankunan karkara a cikin Borno, kuma suna rayuwa a matsayin makiyaya iri daya da ta Fulani.

Sai dai yayin da su Fulani ke yawo da shanu, Kwayam na neman fili don yin noma, wasun su ma har da shanu don yin kiwo