✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An kori sojojin da suka yi sata a Matatar Man Dangote

An kori sojojin nan da aka kama sun saci wayar wutar lantarki a matatar man Dangote daga aiki

Rundunar Sojin Kasa ta Najeriya ta kori sojojinta biyu da aka kama kan satar wayar lantarki a Matatar Man Dangote.

Sojojin da aka kora sun hada da Kofur Innocent Joseph da Las Kofur Jacob Gani wadanda dububsu ta cika bayan sun saci wayar lantarki.

Asirinsu ya tonu ne a hanyar fita daga matatar man, inda sojoji da sauran masu gadi suka kama su a shingen binciken ababen hawa.

Daya daga bisani aka dauka suna hannun hukumar soji domin su fuskanci bincike da kuma ba da nasu bangaren abin da ya faru.

A ranar Litinin bayan kotun soji ta kori sojojin, kakakin rundunar, Onyema Nwachukwu, ya ce an kama su da laifin barin wurin aikinsu.

Manjo-Janar Nwachukwu ya ce a bisa aha da sauran laifukan da aka kama su ne aka more su daga aikin soja nan take.

An kuma Danja su ga hukumomin da suka dace domin gurfanarwa a kotun farar hula domin hakan ya zama darasi ga masu irin wannan hali.