✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An mai da wani kofur din ’yan sanda kurtu

Wani bidiyo ya nuna dan sandan yana kambama wata kungiyar asiri.

Rundunar ’Yan sandan Najeriya ta rage wa wani dan sanda mai suna Isaac Mathew mukami daga kofur zuwa kurtu.

Wani faifan bidiyo a kafar Tik Tok da ke yawo a kafafen sada zumunta ya nuna dan sandan yana kambama wata kungiyar asiri.

Dan sandan yana aiki ne da Rundunar ’Yan sandan Jihar Bayelsa.

Tun ranar 7 ga Mayu ne rundunar ta ga faifon bidiyon. Kuma Kakakin Rundunar ’Yan sandan Najeriya, Olumuyiwa Adejobi ne ya sanar da matakin da aka dauka don ladabtar da jami’in nasu.

Ya ce “An ga Isaac Mathew a faifain bidiyon yana rawa sabe da bindiga kirar AK-47  yana kambama wata kungiyar asiri.”

Ya ce, rundunar ta sha alwashin hukunta duk wani jami’inta da aka samu da aikata laifi irin wannan.