✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An mari Shugaban Faransa a wurin nuna farin jininsa

Wani mutum ya tsinke Shugaba Macron da mari a bainar jama'a.

Wani mai karfin hali ya gaura wa Shugaban Faransa, Emmanuel Macron, mari a bainar jama’a a yayin da Shugaban Kasar yake tsaka da tattakin gwada farin jininsa a kasar.

Tsinka wa Macron mari da mutumin ya yi a cikin cincirindon jama’a ke da wuya, masu tsaron Shugaban Kasar suka cukwikuye shi suka kwato Shugaban Kasar.

Gidan talabijin na BFM da kuma rediyon RMC a Faransar sun ce an kame mutum biyu bisa zargin aikata tsaurin kai.

Firai Ministan Faransa, Jean Castex, ya ce harin da aka kai wa Shugaban ‘takala ce ga mulkin dimokoradiyya’.

Shugaba Macron yana ziyartar yankin Drome da ke Kudu maso Gabashin kasar ne, inda ya hadu da masu gidajen abinci da dalibai domin tattauna yadda za a koma rayuwa kamar yadda aka saba, bayan annobar COVID-19.

A wani bidiyo da ke yawo a shafukan sada zumunta, an gan shi sanye da farar shet yana tafiya a cikin dandazon masoyansa da ke tsaye bayan wani shamakin karfe.

Ya mika hannunsa domin musafaha da wani mutum sanye da koriyar T-shet da tabarau da kyallen rufe hanci a fuskarsa.

Yana dafa mutumin a hannun hagu domin gaisuwa, kawai sai mutumin  ya sa hannunsa na dama ya tsinke shi da mari a fuska.

Fadar Shugaban ta Elysee ta ce an yi yunkurin kai wa Shugaban hari, amma ba ta yi wani karin bayani ba a kai.

A 2016, Macron, wanda a lokacin yana Ministan Tattalin Arziki, an jefe shi a yayin zanga-zanga kan sauye-sauyen kwadago.

Sai dai har lokacin rubuta labarin nan, babu tabbaci kan wane ne mutumin ko kuma dalilinsa na marin Shugaban.