✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An rufe makarantu 50 kan satar jarrabawa a Oyo

26 daga cikin makarantun da lamarin ya shafa na Gwamnati ne, sauran kuma masu zaman kansu.

Gwamnatin Jihar Oyo ta soke lasisin wasu makarantun sakandare 50 a jihar bayan samunsu da hannu a magudin jarrabawa.

Ma’aikatar Ilimi ta jihar ta sanar a ranar Alhamis cewa, an sami makarantun da tafka magudi a yayin Jarrabawar Kammala Karatun Sakandire ta WAEC a bana.

Jaridar Intelregion ta rawaito cewa makarantu 26 daga cikin wadanda lamarin ya shafa na gwamnati ne, sauran kuma masu zaman kansu.

Daga cikin makarantun da aka rufe akwai; Community High School da Ajia Mount Sinai Coll Adegbayi da Ilupeju Community High School da Alugbo Osegere Olukeye Community High Sch.

Sai kuma Ibadan City Model College da Ibadan Mollyvonne College da Owo Community Grammar School da Owo Progressive Secondary Gramm School da sauransu.