✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An rufe makarantu 56,000 a Pakistan saboda ciwon ido

Gwamnatin kasar ta ce za ta fitar da sanarwar ranar da za a sake bude makarantun.

Fiye da makarantu 56,000 aka rufe a kasar Pakistan, a wani yunkuri na dakile yaduwar ciwon ido mai saurin yaduwa, in ji jami’an kasar a ranar Laraba.

Miliyoyin dalibai ne dai za su zauna a gida daga ranar Alhamis bayan da yankin Punjab, lardin da ya fi yawan jama’a a kasar, ya ba da sanarwar rufe makarantu.

Hakan dai ya biyo bayan kamuwar da mutum 357,000 suka yi da cutar tun farkon shekarar nan.

Ciwon ido da ke saurin yaduwa yana sanya ido ya yi ja, yana sanya zazzabi da zubar da jini daga idanu kuma cutar na iya yaduwa ta hanyar hada hannu, da kuma tari ko atishawa.

Kakakin Ma’aikatar Ilimi ta Punjab Zulfiqar Ali, ya shaida wa AFP cewa “An sanar da rufe makarantun a matsayin wani mataki na samar da kariya ga dalibai daga kamuwa da cutar.”

Akwai mazauna 127,000,000 a gabashin lardin Punjab da makarantun jiha 56,000, da kuma dubunnan makarantu masu zaman kansu su ma sun rufe.

“Muna fatan wannan zai karya tasirin kamuwa da cutar a lardin,” in ji Ali.

An riga an rufe makarantu a duk fadin Pakistan a ranar Juma’a har zuwa lokacin da gwamnatin a kasar za ta fitar da sabuwar sanarwa

Hukumomin Punjab sun ce za a tantance daliban a kofar makaranta idan sun sake bude makarantun nan gaba.