An sace magidanci a hanyar kai dansa jarabawar JAMB | Aminiya

An sace magidanci a hanyar kai dansa jarabawar JAMB

Mahara
Mahara
    Usman A. Bello, Benin da Abubakar Muhammad Usman

Wasu ’yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun sace wani magidanci a yayin da yake kai dansa zana jarabawar JAMB domin neman gurbin shiga manyan makarantu a Jihar Edo.

Bayanai sun nuna lamarin ya faru sa misalin karfe 7 na safiyar ranar Asabar a kan babban titin Benin zuwa Legas a Karamar Hukumar Ovia ta Arewa Maso Gabas, a Jihar Edo.

Rahotanni sun ce magidancin ya dauki dansa zai kai shi cibiyar zana jarabawar ta JAMB ne a kan babur din haya, daga bisani maharan suka yi awon gaba da shi.

An gano cewa bayan maharan sun sace magidancin shi kadai, sai suka bar dan a inda abin ya faru.

Kakakin ’yan sandan Jihar Edo, Bello Kontongs, ya tabbatar mana cewa maharan sun sace mutumin ne a lokacin da yake kai dansa inda zai zana jarabawar ta JAMB.

Sai dai ya ce tuni aka baza ’yan sanda a dajin don ceto magidancin daga hannun maharan ba tare da wani abu ya same shi ba.