✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace tsohon Shugaban Karamar Hukuma a Taraba

’Yan bindigar neman Naira miliyan 30 a kan mutum ukun da suka yi garkuwa da su.

’Yan bindiga wadanda ake kyautata zaton masu satar mutane don karbar kudin fansa sun yi awon gaba da tsohon Shugaban Karamar Hukumar Ardo-Kola da ke Jihar Taraba tare da wasu mutum biyu.

Wannan lamari ya auku ne da misalin karfe bakwai na dare ranar Asabar a kan hanyar Bali zuwa garin Takum.

Majiyar Aminiya ta ce tsohon Shugaban Karamar Hukumar mai suna Alhaji Tanimu Umar yana kan hanyarsa ce tare da wasu mutum biyu daga garin Takum zuwa Jalingo ’yan bindigar suka tsare su a wata kwana kusa da garin Jatau da ke cikin Karamar Hukumar Bali.

Ta tabbatar wa wakilinmu cewa ’yan bindigar sun haura da Alhaji Tanimu da sauran mutanen wani tsauni inda har yanzu suke tsare da su.

Majiyar ta ce wadanda suka sace wadannan bayin Allah sun nemi a ba su Naira miliyan 10 a matsayin kudin fansa akan kowanne mutum daya, jimilla Naira miliyan 30 ke nan.

Ta kuma shaida wa wakilin Aminiya cewa har yanzu ba a daidaita ba kan adadin kudin da masu garkuwar ba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar Taraba, DSP David Misal ya shaida wa Aminiya cewa lamarin ya auku ne a ranar hutun karshen mako don haka bai riga ya samu sami cikakken bayanin yadda abin ya auku ba a lokacin da Aminiya ta tuntube shi.

Wata makamanciyar wannan, Gwamnan Jihar Taraba Darius Ishaku ya yi alkawarin cewa gwamnatin jihar za ta taimaka wajen ganin an kubutar da wani dan kasar Sin da aka sace tare da direbansa a Karamar Hukumar Donga a makon jiya.