✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sace tsohuwa mai shekara 70 da wasu mutum 10 a Taraba

Masu garkuwar dai na neman a biya su Naira miliyan 70.

Akalla mutum 11 ne wasu ’yan bindiga suka sace a kauyen Illela da ke Karamar Hukumar Karim Lamido a Jihar Taraba.

Wata majiya ta shaida wa Aminiya cewa da misalin karfe 4:00 na safiyar Alhamis ne ’yan bindigar suka auka wa kauyen sannan suka sace mutanen, cikin su har da wata tsohuwa mai kimanin shekarar 70 mai suna Zainab Adamu.

Majiyar, ta shaida wa wakilinmu cewa tsohuwar ta rasu ne a hannun ’yan bindigar, yayin da biyu daga cikin mutanen da aka sace suka kubuta daga inda aka boye su.

Har ila yau, daga cikin mutanen da aka sace har da dan Dagacin garin Zip.

Dagacin, Alhaji Uba, ya shaida wa wakilinmu cewa dan nasa Mai suna Buhari na daga cikin mutanen da aka sace a yayin harin.

Sai dai ya ce har har yanzu yana hannun wadanda suka sace shi.

Alhaji Uba ya ce ’yan bindigar dai sun bukaci a biya su kudi har Naira miliyan 70 a matsayin kudin fansa.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan Jihar, DSP Usman Abdullahi, ya tabbatar da faruwar harin, kodayake bai yi karin haske a kai ba.