✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An sace tsohuwa mai shekara 80 a Makarfi

An sace Hajiya Maude da wasu magidanta biyu da matashi daya.

Rahotanni sun tabbatar da cewa ’yan bindiga sun sace mutum hudu a Kauyen Rahaman Wali da ke Karamar Hukumar Makarfi a Jihar Kaduna.

Tsohuwar wacce ta haura shekara 80 a duniya mai suna Hajiya Maude Mamman,  na daga cikin mutum uku da ’yan bindigar suka yi garkuwa da su.

Aminiya ta ruwaito cewa, lamarin ya auku ne da misalin karfe 1:30 na daren Lahadi, 26 ga watan Yulin da muke ciki.

Bayanai sun ce gungun masu satar mutane da neman kudin fansa dauke da miyagun makamai sun auka kauyen ne inda suka sace Hajiya Maude da wasu magidanta biyu da matashi daya.

Sauran wadanda aka sace sun hada da wani Malam Murtala Nazifi, wanda ke aiki a Asibitin Kula da Masu Tarin Fuka da Cutar Kuturta da ke Zariya, da Alhaji Nuhu, Ma’aikaci a Matatar Mai (Refinery) sai kuma wani mai suna Kabiru, da ke zaman dan uwan Alhaji Nuhu.

Wakilinmu ya ziyarci Rahaman Wali, inda ya tarar da mutane kauyen cikin firgici da jimami dangane da faruwar lamarin da ya bar su cikin zullumi.

Sai dai an samu sabanin bayanai yayin da kowa ke furta albarka cin bakinsa dangane da yadda lamarin ya auku, yayin da kuma wadansu suka ce ba za su yi saurin furta wani abu a kai ba.

Aminiya ta samu cewa, galibi mutanen kauyen da aka nemi jin ta bakinsu a kan lamarin sun ce lokacin magana bai yi ba saboda ba su da masaniya kan halin da wadanda aka sace suke ciki.

Sai dai wata majiya da ta nemi a sakaya suna ta ce, an fara magana da wadanda suka sace mutanen kauyen, kuma har sun bukaci Naira miliyan goma a matsayin kudin fansa.

Duk kokarin jin ta bakin Kakakin Rundunar ’yan sanda Jihar Kaduna, ASP Mohammed Jalige, abin ya ci tura don bai daga wayarsa ba.