✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sake gano yaran da aka sace daga Kano a Anambra da Enugu

An gano su ne bayan ya kai ziyara wasu gidajen raino a jihohin Anambra da Enugu.

Gwamnatin Jihar Kano ta ce an sake gano karin yaran da ake zargin an sace daga jihar a jihohin Anambra da Enugu.

Kwamishinan Watsa Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba ne ya tabbatar da hakan a wata hirarsa da Sashen Hausa ba BBC ranar Litinin, inda ya ce tuni ma wasu daga cikin iyayensu suka gane su.

Ya ce kwamitin da gwamnatin jihar ta kafa ta kuma dorawa alhakin nemo yaran ne ya gano su bayan ya kai ziyara wasu gidajen raino a jihohin Anambra da Enugu.

“Bayan mun gano su sai muka dauki hotuna da bidiyonsu muna cigiyar iyayensu, cikin ikon Allah har biyar daga cikin iyayen yaran sun gane ‘ya’yan nasu,” inji Kwamishinan.

Ya ce yanzu haka kwamitin ya dukufa wajen tantance ikirarin wasu iyaye a kan yaran domin gudun sake yin daben kwalo.

Malam Muhammad Garba ya tabbatarwa da iyayen yaran cewa nan ba da jimawa ba za a dawo musu da dukkan yaran nasu.

A shekarar 2019, Rundunar ‘Yan Sanda ta Jihar Kano ta cafke wani mai suna Paul da matarsa Mercy wadanda aka zarga da sace yaran daga Kano zuwa Anambra, tare da canza musu suna da addini.

Ko a kwanakin bayan sai da wasu iyaye mata suka gudanar da zanga-zanga a jihar kan abinda suka kira jan kafar da gwamnatin jihar ke yi wajen sake sada su da yaran duk da gano sun da aka yi tsawon lokaci.