✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sako karin daliban FGC Birnin Yauri

Iyaye na tattauna da ’yan bindiga a cikin daji don ganin an sako ragowar daliban da ke hannunsu

Bayan shekara biyu, ’yan ta’adda sun sako hudu daga cikin ragowar daliban Makarantar Sakandaren Gwamnatin Tarayya (FGC) da ke Birnin Yauri a Jihar Kebbi da ke hannunsu. 

Aminiya ta ruwaito cewa a ranar Karamar Sallah da dare ne jagoran ’yan bindiga, Dogo Gide, ya sako karin daliban daga cikin 11 da suka rage a hannunsu.

Wadanda aka sako din su ne: Bilha Musa da Faiza Ahmed da Rahma Abdullahi da kuma Hafsa Murtala.

Shugaban kungiyar iyayen daliban da aka sace, Salim Kaoje, ya shaida mana cewa, “Sai da aka kwana shida ana tattaunawa a cikin daji kafin aka sako mana yaran.

“Saura ragowar yara bakwai da wasu mutum biyu daga cikin iyaye suke cikin daji suna kokarin ganin an sako su.”

Salim Kaoje ya bayyana cewa sai da suka biya kudin fansa kafin a sako daliban, kuma kadarorin iyayen suka sayar suka tara kudin da taimakon wasu ’yan Najeriya domin biyan kudin fansan.

Idan ba a manta ba a watan Janairu Kaoje ya tabbatar cewa suna tattaunawa da Dogo Gide, bayan da suka samu mahaifiyar dan ta’addan ta sa baki domin ya sako su.

A ranar 17 ga watan Yunin 2021 ne ’yan ta’adda suka kai hari a makarantar kwana ta FGC Birnin Yauri, mallakin Gwamnatin Tarayya, suka sace daliban.

Daga baya suka sako daliban, amma suka ci gaba da rike wasu guda 11, duk kuwa da cewa an biya makudan kudade da kuma musayar daliban da wasu ’yan bindiga da ke hannun gwamnati a lokuta daban-daban.