✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An samu sabuwar ɓaraka tsakanin mawaƙan Kannywood?

Aminiya ta lura a cikin kungiyar Murya Daya akwai mawakan tsagin YBN da 13×13 da Kwankwasiyya a ciki.

A farkon makon nan ne Kungiyar Murya Daya, wadda wata sabuwar kungiyar mawakan Kannywood ce ta ziyarci tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.

Kungiyar a karkashin jagorancin shugabanta, mawaki Ali Jita sun ziyarci tsohon Shugaban Kasa ne a gidansa da ke Daura a Jihar Katsina domin nuna masa goyon baya da girmamawa.

Wannan ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake cigaba da caccakar mawaki Dauda Kahutu Rarara a bisa wasu kalamai da ya yi da ake ganin kamar butulci ne ga tsohon Shugaban Kasa Buhari.

Aminiya ta ruwaito mawaki Dauda Kahutu Rarara a yayin wani taron manema labarai yana zargin cewa tsohon shugaban da lalata kowanne fanni na Nijeriya kafin ya mika mulki Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu a watan Mayu da ya gabata.

Mawakin ya kuma nuna nadamarsa ta goyon bayan Buharin a baya, inda ya ce ya yi da-na-sanin yin hakan.

A cewarsa, “Na yi nadamar goyon bayan Buhari, saboda na yi zaton zai gyara Nijeriya, amma hakan ba ta samu ba. Buhari ya gurgunta dukkan hukumomin gwamnati, dole sai an farfado da su.”

Ya kuma ce hatta wata uku na farkon mulki Tinubu, sun fi shekaru takwas na mulkin Buhari.

Mawakin ya kuma ce hatta a kan batun nadin ministoci a gwamnatin, kamata ya yi a ce an nemi shawararsa kafin a nada su.

Rarara ya ce akalla idan ma ba a ba shi kujerar Minista ba, to kamata ya yi a ce an yi kasafinsu da shi. Ya kuma yi zargin cewa an nada makiyan Tinubu da dama mukamai a cikin kunshin gwamnatinsa.

Rarara ya kuma bigi kirjin cewa a duk fadin Arewacin Nijeriya, idan ban da tsohon Gwamnan Kano, Abdulahi Umar Ganduje da na Katsina, Aminu Bello Masari, babu wanda ya ba tafiyar Tinubu gudunmawa kamar shi.

Sai dai tun a lokacin tsohon hadimin tsohon Shugaba Buharin, Malam Bashir Ahmad ya fito ya mayar da martani ga mawakin.

Sai dai jim kadan bayan wadannan kalamai na Rarara, sai mutane suka yi ca a kan mawaka, inda mutane da dama suka kwatanta su da maciya amana, butulu.

Hakan ya sa aka rika caccakar Rarara da sauran mawakan baki daya, wanda watakila hakan na da nasaba da wannan ziyara ta Murya Daya.

Kafin ziyarar, kungiyar ta kira taron manema labarai, inda ta barranta kanta daga kalaman mawakin.

A cewar Ali Jita, “mun kira wannan taron manema labaran ne domin warware zare da abawa a kan kalaman da wani daga cikinmu mawaka na Arewa ya yi.

“Mu a matsayinmu na kungiyar Murya Daya, mun nazarci wadannan kalamai da wannan mawaki ya yi da suka jawo ce-ce-ku-ce musamman a kafofin sadarwa, wanda hakan ne ya tilasta mana mu fito mu nesanta kanmu daga wadannan kalamai da ya yi.

“Al’umma su sani ya yi kalaman ne a madadin kan shi, kuma ba ma tare da shi,” inji Ali Jita.

Da yake kara bayani, mawaki El-Mu’az Birniwa ya bayyana cewa su a matsayinsu na mawaka ’yan Arewa, ba za su laminci cin mutuncin duk wani dattijon Arewa ba, sannan ya yi kira da a daina yi wa mawallafa baki daya kudin guru a kan laifin guda daya.

Aminiya ta ruwaito cewa kafin zabe, mawakn sun kasu gida biyu, inda akwai mawaka karkashin jagorancin Abdul Amart Maikwashewa da kungiyarsa ta YBN, da kuma mawakan 13×13 karkashin mawaki Dauda Kahutu Rarara.

Adawa ta yi zafi sosai a tsakaninsu kafin, inda ba a ganinsu a tare a waje daya, ko kuma ko da sun zo taron, kowane bangare yakan ware ne ya yi na shi wasan.

Sannan kuma akwai mawakan Kwankwasiyya da suke gefe guda su kuma, musamman a siyasar Kano.

Aminiya ta lura a cikin kungiyar Murya Daya akwai mawakan tsagin YBN da 13×13 da Kwankwasiyya a ciki.

Kwanaki kadan bayan ziyarar da Murya Daya ta kai wa tsohon Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, sai daya daga cikin manyan na hannun mawaki Dauda Kahutu Rarara, darakta Aminu S. Bono ya sanya hoton Rarara, sannan ya rubuta shafinsa na Instagram, “Saura ’yan kwanaki kadan zan yi rubutu a kan wannan bawan Allah, ina fatan wanda zan saba wa ya yi hakuri amma zallar gaskiya zan fada cikin fahimta ta.”

Sai dai wasu sun nuna farin ciki da cewa suna jiransa, amma wasu suka bayyana masa cewa su dai ba za su taba yarda da shi ba.

Wani mai suna Aminu Ibrahim ya rubuta cewa, “Ya fi kyau da ka ce a fahimtarka, ka ga kuwa fahimtarka ba lallai ta zamo gaskiya ba.

“Watakila kuma ka kawo son zuciya a cikin lamarin kasancewar kai yaronsa ne, ba zai yiwu ya yi wani abu wanda ba daidai ba ka iya nuna wa sakamakon kana tunanin zai yanke maka wani jin dadi daga bangarensa amma gaskiya ba ta canja wa komai rintsi. Allah Ya kiyaye,” inji shi kamar yadda ya rubuta a kasan rubutun na Aminu Bono.