✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An sauya tsarin bayar da kyautar Ballon d’Or

Za a rika ba da kyautar bisa wasannin da aka yi tsawon kakar wasa guda a nahiyyar Turai.

Mahukuntan da ke bayar da kyautar gwarzon dan wasa ta Ballon d’Or, sun sauya tsarin tantance wadanda za su rika lashe kyautar.

Mujallar wasanni ta France Football da ke bayar da kyautar tare da hadin gwiwar Hukumar Kwallon Kafar Faransa ne suka sanar da hakan a karshen makon da ya gabata.

Wannan na zuwa ne a sakamakon martani ga sukar kyautar ballon d’Or ta shekarar 2021 da aka bai wa Lionel Messi a karo na bakwai, wadda masu sharhi da dama ke ganin dan wasan gaban Bayern Munich Robert, Lewandowski ya cancanci lashe ta.

Daga yanzu za a rika ba da kyautar ta Ballon d’Or ne bisa wasannin da aka yi a tsawon kakar wasa guda a nahiyyar Turai, a maimakon shekara guda wato daga Janairu zuwa Disamba.

An kuma rage yawan alkalan da za su zabi wanda zai lashe kyautar zuwa ’yan jarida kimanin 100, a maimakon 170 da ake amfani da kuri’unsu a baya.

Yayin da a ajin mata, ’yan jarida 50 za su rika aikin tantancewar.

Kazalika, lokacin mika kyautar ta Ballon d’Or kuwa, an sauya shi ne zuwa watan Satumba ko Oktoba, bisa la’akari da kakar wasan da ta kare a watan Yuli tare.

Hakan na nufin taurarin da suka yi bajinta a gasar Cin Kofin Duniya da za ta gudana a Qatar cikin watannin Nuwamba da Disamba, za su jira har zuwa shekarar 2023 ne kafin samun damar lashe kyautar ta gwarzon dan wasa.