✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tabbatar da Nababa a matsayin Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Yari

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin Mista Haliru Nababa, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Yari ta kasa. Tabbatar da nadin Nababa…

Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da nadin Mista Haliru Nababa, a matsayin sabon Shugaban Hukumar Kula da Gidajen Yari ta kasa.

Tabbatar da nadin Nababa ya biyo bayan rahoton da Kwamitin Majalisar kan harkokin cikin gida ya gabatar yayin zamanta na ranar Laraba.

Aminiya ta samu cewa Shugaban Kwamitin, Sanata Kashim Shettima mai wakiltar shiyyar Borno ta Tsakiya, shi  ne ya gabatar da rahoton.

Shettima wanda ke zaman tsohon Gwamnan Jihar Borno, ya bayyana wanda aka nada a matsayin jajirtaccen mutum, wanda zai yi aiki tukuru wajen ciyar da hukumar gaba.

Ya ce babu wani koke da aka gabatar game da nadin Nababa don haka ya bayar da shawarar a tabbatar da shi.