✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tabbatar da Usman Baba a matsayin Shugaban ’Yan Sanda

Majalisar Harkokin ’Yan sanda ta tabbatar da shi a matsayin cikakken Shugaban ’yan sanda.

Majalisar Harkokin Dan Sanda ta tabbatar da Usman Alkali Baba a matsayin cikakken Babban Sufeton ’Yan Sandan Najeriya.

An tabbatar da nadin nasa ne a zaman Majalisar da Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya jagoranta a ranar Juma’a.

Ministan Harkokin ’Yan Sanda, Muhammad Maigari Dingyadi, ya ce Buhari ya umarci Shugaban ’Yan Sandan ya tabbatar da ganin an samu gabala a kan matsalar tsaro da ke ci wa Najeriya tuwo a kwarya.

Dingyadi ya ce Majalisar ta amince da nadin ne bisa la’akari da nasarorin sabon Sufeto Janar din ya samu da kuma gogewarsa ta aiki.

A ranar 6 ga Afrilu ne Shugaban Buhari ya amince da nadin Usman Baba a matsayin mukaddashin Shugaban ’Yan Sanda.