✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsare tsohon Ministan Equatorial Guinea saboda sukar Shugaban Kasar

Yanzu sati Uku ke nan yana tsare a hannunsu

Kasar Equatorial Guinea ta tsare tsohon Ministan Shari’a na Kasar bayan ya caccaki Shugaban Kasar,  kamar yadda dan uwansa da ‘yan adawa suka sanar a ranar Alhamis.

Sun ce yau kusan mako uku ke nan babu shi babu labarinsa.

Shugaba Teodoro Obiang Nguema Mbasogo, mai shekara 80, ya shafe fiye da shekara 43 yana mulkin Equatorial Guinea , wanda hakan ya sa ya zama shugaban da ya fi dadewa a kan karagar mulki a duniya.

An kama tsohon Ministan, Ruben Maye Nsue Mangue, mai shekara 59 a daren bakwai ga watan Agustan 2022, a garin Mongomo da ke Gabashin kasar.

Kamun na shi ya faru ne lokaci da aka kira shi wajen taron da jam’iyya mai mulkin kasar ta yi, kamar yadda daya daga cikin ’yan uwansa Ruben Monsuy ya shaida wa Kamfanin Dillancin Labarai na Faransa, AFP.

Ya ce, “Bayan taron, an kama Ruben kuma an tafi da shi wani wuri da ba a sani ba bayan ya ki ya nemi afuwar Shugaban Kasa,” inji shi.

Ya ce yanzu ba su da masaniyar inda yake.

Ma’aikatun Yada Labarai da ta Shari’ar kasar ba su mayar da martani nan take ba kan bukatar jin ta bakinsu da AFP ya yi ba.

Kwanaki biyar bayan kama tsohon Ministan wanda kuma limamin coci ne, Ma’aikatar Shari’ar ta ba da umarnin hana shi yin wa’azi tare da zarginsa da ‘tunzura jama’a’.

A ranar 25 ga watan Yulin 2022, tsohon Ministan Shari’a a cikin sakon murya na manhajar Whatsapp wanda ya yi ta yawo ya soki yadda Shugaban Kasar ke tafiyar da harkokin kasar, yana mai bayyana shi a matsayin “aljani… mai rike da al’ummarsa kamar fursunoni”, da kuma kiran a yi tattaunawa ta kasa.

Gamayyar jam’iyyun adawa da kungiyoyin fararen hula da masu sa ido kan kare hakkin bil’adama sun tabbatar da kamun tsohon Ministan.

Ruben Maye ya kasance Ministan Shari’a a kasar daga shekarar 1998 zuwa 2004, sannan aka nada shi Jakada a Amurka a shekarar 2013.