✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An tsinci gawar jariri da aka jefar a juji a Jigawa

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Civil Defence (NSCDC) reshen Jihar Jigawa, ta sanar da tsinto wani mataccen jariri da aka yasar a juji a Dutse,…

Hukumar Tsaron Farin Kaya ta Civil Defence (NSCDC) reshen Jihar Jigawa, ta sanar da tsinto wani mataccen jariri da aka yasar a juji a Dutse, babban birnin Jihar.

Kakakin Hukumar a Jihar, Mista Adamu Shehu ne ya inganta rahoton yayin zantawarsa da Kamfanin Dillancin Labari na Kasa (NAN) ranar Litinin da birnin Dutse.

Shehu ya ce ’yan jari-bola ne suka tsinci gawar jaririn a Unguwar Takur da misalin karfe 10.30 na safiyar ranar Lahadi da ta gabata.

A cewarsa, “A ranar Lahadi, 16 ga Mayun 2021, na amsa kiran waya daga wani mai gyaran famfo mazaunin Unguwar Takur a garin Dutse, da cewa an tsinci wani abu mai kama da mataccen jariri da aka jefar da shi cikin wani buhu.

“Wasu samu samari ’yan jari-bola ne suka tsinto gawar jaririn yayin da suke tsince-tsince a wata juji.

“Nan take muka aika jami’am zuwa wurin da abin ya faru, inda suna isa suka gano jajirin da tuni wutar da ke ci a jujin ta kone wani sashe na jikinsa.

“An mika gawar jajirin ga Dagacin yankin, Malam Bashir Tukur Jinjiri domin yi masa jana’iza,” a cewarsa.

A yayin da suke ci gaba da gudanar da bincike, Kakakin ya ce ya zuwa yanzu babu wanda aka kama da ake zargi da aikata laifin.

Kazalika, ya ce Kwamandan Hukumar NSCDC na Jihar, Alhaji Garba Muhammad, ya tir da faruwar lamarin tare da bayar da umarnin a fadada bincike domin zakulo duk wanda ya aikata laifin.