✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An tsinci gawar matashi a cikin kwata a Kano

Wannan ita ce gawa ta uku da ake tsinta a wajen cikin kwana 3

An tsinci gawar wani matashi mai kimanin shekaru 25 mai suna Ghaddafi Saleh a cikin wata kwata da safiyar Laraba a Jihar Kano.

Lamarin ne a unguwar Kundila kan titin Zariya daura da asibitin dabbobi.

A zantawar Aminiya da wani matashi kuma mazaunin yankin, Sultan Bello, ya ce ruwa ne ya koro gawar mutumin ya kawo ta wannan waje.

Ya kuma ce, “Wannan ba shi ne karo na farko ba da ake tsintar irin wannan gawar, na uku ke nan cikin kwanaki hudu da suka wuce.”

A nasa bangaren, mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusuf Abdullahi, ya tabbatar da rasuwar matashin, inda ya ce tuni suka mika gawar ga ofishin ’yan sanda da ke Titin na Zariya Road a Kano.

Ya kara da cewar mamakon ruwan da aka yi ranar lahadi shi ne musabbabin faruwar hakan.