✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Sakamakwon Zaben Gwamnonin Najeriya Na 2023 (Alkaluma Daga:INEC)

An yanke wa ’yan adawa 47 hukuncin dauri a Kamaru

An yanke hukuncin kan ’yan adawar kan zargin yin tawaye ga gwamnatin kasar.

Wata kotu a kasar Kamaru ta yanke wa wasu masu adawa da gwamnatin kasar 47 hukuncin zaman gidan yari, bayan samun su da laifin yi wa kasar tawaye.

Daga cikin wadanda aka yanke wa hukuncin har da magoya bayan madugun adawar kasar, Maurice Kamto, wadanda suka hada da mai magana da yawunsa da ma’ajin jam’iyyar adawa ta MRC da sauransu.

An yanke wa mutum 47 din an yanke musu hukuncin daurin shekara daya har zuwa shekara bakwai a gidan gyaran hali.

Tun a ranar 22 ga watan Satumbar 2020 ne aka cafke wadanda aka yanke wa da hukuncin, a lokacin da suka gudanar da zanga-zangar adawa da shugaban kasar, Paul Biya.

Sun gudanar da zanga-zangar ne don neman Mista Paul Biya ya sauka daga karagar mulki, bayan shafe tsawon shekara 39 yana mulkar kasar.

Jam’iyyar adawa ta MRC a kasar na zargin jami’an tsaro da amfani da karfin tuwo wajen tarwatsa masu zanga-zangar lumana tare da kame sama da mutum 500.

Kuma jam’iyyar ta ce har yanzu hukumomin tsaron kasar na tsare da akalla mutum 124 wadanda suka fito domin gudanar da zanga-zangar lumana.