Daily Trust Aminiya - Laporta ya sha alwashin dawo da Guardiola Barcelona
Subscribe

Pep Guardiola

Laporta ya sha alwashin dawo da Guardiola Barcelona

Kafafen yada labarai a Spaniya sun rawaito tsohon shugaban kungiyar kwallon kafa ta Barcelona, Joan Laporta, yana shan alwashin dawo da Pep Guardiola kungiyar.

Ya sha alwashin dawo da tsohon kocin na Barcelona ne dai idan ya yi nasarar sake zama shugaban kungiyar a zaben da za a gudanar a badi.

Laporta ne shugaban kungiyar Barcelona daga shekarar 2003 zuwa 2010 lokacin da aka dauko Guardiola daga horar da kungiyar matasa zuwa gurbin kwararru.

A halin yanzu dai, Guardiola yana da kwantiragi a kungiyar Manchester City har zuwa watan Yunin shekarar 2021.

Makomar shi ta shiga rudani tun bayan da Hukumar Kwallon Kafa ta Turai (UEFA) ta dakatar da kungiyar ta Manchester City na tsawon shekara biyu daga shiga Gasar Turai bisa laifin ketare ka’idojin kashe kudi.

Tuni dai kungiyar ta daukaka kara a kan lamarin.

Tashar talabijan ta TV3 da ke yankin Kataloniya ta rawaito Laporta yana cewa, “Ina aiki tukuru saboda gabatar da kaina a matsayin dan takarar shugabancin kungiyar. Na taba zama shugaban kungiyar kuma zan yi farin ciki idan na dawo.

“Zan yi matukar farin ciki idan Guardiola ya dawo kungiyar, amma a yanzu yana City kuma Pep shi kadai yake da ikon yanke hukunci a kan hakan.

“Shi zakaran gwajin dafi ne a Barcelona kuma da yawa daga cikin mutanen Kataloniya za su so a ce ya dawo Barca.

“Idan lokaci ya yi, zan tattauna da wanda muke tunanin zai zama kociyan Barca daga shekarar 2021”.

Kungiyar Barcelona ta lashe gasar wasanni 14 wadanda suka hada da La Liga uku da Gasar Zakarun Turai biyu a karkashin jagorancin Guardiola kafin barin sa kungiyar a shekarar 2012.

Annobar coronavirus dai ta tilasta dakatar da wasanni a kasar Spaniya.

Barcelona ta fada a cikin rudani tun lokacin da daraktoci shida suka yi murabus daga kungiyar a watan Afrilu saboda rashin amincewa da yadda ake gudanar da ita.

More Stories