✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi amfani da sa hannun Buhari na bogi wajen cire Dala 6.2m daga CBN —Boss Mustapha

Boss Mustapha ya ce ba daga ofishinsa ko fadar shugaban kasa takardar da aka yi amfani da ita wajen cire kudaden ta fito ba

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, ya musanta ba da izinin biyan Dala miliyan 6.2 ga masu sanya ido kan harkokin zaɓe na ketare.

Boss Mustapha ya bayyana hakan ne a gaban wata babbar kotu da ke Abuja a inda ya shaida mata cewa, ba shi da masaniya kan wata takardar ba da izini ga tsohon Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN) Godwin Emefiele, wadda ake zargin ta sahale masa biyan sama da Dalar Amurka miliyan 6.2 ga masu sanya ido a zaɓe na ƙasashen waje.

Tsohon Sakataren Gwamnatin wanda yana daga cikin shaidu a ƙarar da ake tuhumar Emefiele ya ce, a tsawon shekara biyar da wata bakwai da ya yi yana riƙe da wannan muƙamin, ba shi da masaniya kan takardar.

Boss Mustapha ya kuma bayyana wa kotun cewa, ba daga ofishinsa takardar ta fito ba kuma ba daga fadar tsohon Shugaban Kasa, Muhammadu Buhari takardar biyan kuɗaɗen ta fito ba.

Tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya ya kuma shaida wa kotun cewa, babu ruwan Gwamnatin Tarayyar da biyan masu sa-ido na ƙasashen wajen kuɗaɗe.

A ƙunshin takardun bayanan da jagoran lauyoyin masu kara, Rotimi Oyedepo suka gabatar masa, tsohon Sakataren Gwamnatin ya ce, bai taba ganin su ba, hasali ma sa hannun da suke ɗauke da su na Buhari na jabu ne, sai dai ya bar wa kwararru hakan su tabbatar.

Mista Emefiele dai na fuskantar tuhume-tuhume 20 a shari’ar, waɗanda suka haɗa da cin hanci da rashawa, haɗa baki domin aikata laifi, da cin amana da ungulu da kan zabo da kuɗaɗen da suka kai dalar Amurka $6,230,000.

Ana zargin tsohon Gwamnan na CBN da yin amfani da sa hannu na jabu domin karɓar kuɗaɗen ba bisa ƙa’ida ba.

Masu sa-ido a babban zaben ƙasar da aka yi a 2023 na ƙasashen waje ake ikirarin an biyan kuɗaɗen.