✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da amarya a hanyar gidan miji

‘Yan bindiga sun sace wata amarya a hanyar kai ta gidan mijinta bayan daurin aure tare da wata mai shayarwa a Jihar Sokoto. Maharan sun…

‘Yan bindiga sun sace wata amarya a hanyar kai ta gidan mijinta bayan daurin aure tare da wata mai shayarwa a Jihar Sokoto.

Maharan sun yi dauke amaryar ce a ranar Laraba, ranar da aka yi garkuwa da wasu ‘yan kasuwa da ba tantance adadinsu ba a kan hanyar Balle-Tangaza.

“Motocin ‘yan kasuwar sun ci karo da shingen da ‘yan bindidan suka sanya; suka umarce su da su fito, suka shige da su ikin daji da su.

“Har zuwa ranar Juma’a babu labarinsu amma an bar motar a wurin da aka dauke su”, inji majiyarmju.

A ranar Alhamis ne ‘yan bindiga suka dauke matar Magajin garin Sulli da diyarta da take shayarwa, duk a Karamar Hukumar Tangaza.

Direban daya daga cikin motocin ‘yan kasuwar da ‘yan bindigar suka harba ya samu sauki, dayan kuma ya mutu.

Wakilinmu ya ce mazauna sun yi kaura daga wasu kauyukan da ke yankin saboda gudun a kawo musu hari.

“Akwai wani kauye mai suna Garin Alfarma; yawancin ‘yan kauyen sun tsere zuwa Gidan Madi, hedikwatar Tangaza saboda tsoron ‘yan bindiga”, kamar yadda ta ce.

Wata majiyar tsaro ta ce ana yawan garkuwa da mutane a kananan hukumomin Tangaza da Gudu a baya-bayan nan musamman da dare.

“Sun fi zuwa su yi garkuwa da mutane a wurare masu nisa da ba za mu iya kaiwa ba a kan kari saboda yanayin hanyoyin.

“Ko yau sai da muka kama wasu da ake zargin ‘yan bindiga ne da masu yi musu leken asiri a Gudu”, inji shi.

Kakakin Rundunar ‘Yan Sandan Jihar Sokoto ASP Muhammad Sadiq ya tabbatar da faruwar hakan, ya kuma ce ana yin sintirin hadin gwiwa a yankunan.

“Mun tsaurara matakan tsaro domin kare yankin da kama ‘yan bindigar da kuma kubutar da mutanen da suka sace”, inji shi.