Daily Trust Aminiya - An yi garkuwa da mai juna biyu a Taraba
Subscribe

An yi garkuwa da mai juna biyu a Taraba

’Yan bindiga ne sun yi garkuwa da wata mata mai juna biyu da wata mata da talatainin dare a Karamar Hukumar Lau ta Jihar Taraba.

Mai cikin da aka yi awon gaba da ita da misalin 2.30 na dare matar wani dan kasuwa a yankin.

Wata majiya a garin Lau ta shaida wa Aminiya cewa kafin a yi garkuwa da matar sai da ’yan bindigar kusan goma dauke da muggan makamai suka shiga yankin.

Ko a makon da ya gabata an yi garkuwa da mutum bakwai cikinsu har da tsohon dan Majalisar Dattawa a jihar ta Taraba.

Kakakin Rundunar ’Yan Sandan jihar DSP David Misal ya ce yana jiran samun rahoto daga ofishin ’yan sandan da ke Lau game da abin da ya faru.

More Stories