✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi garkuwa da Sarkin Bungudu

An yi garkuwa da basaraken a hanyar Kaduna zuwa Abuja.

’Yan bindiga sun yi garkuwa da Sarkin Bungudu na Jihar Zamfara, Alhaji Hassan Attahiru.

An yi garkuwa da Sarkin Bungudu ne a ranar Talata a Babban hanyar Abuja zuwa Kaduna  bayan musayar wutar da masu tsaron basaraken suka yi ’yan bindigar.

Rundunar ’Yan Sadan Jihar Kaduna, cikin wata sanarwar da ta fitar a daren Laraba ta tabbatar da garkuwa da basaraken, mai daraja ta daya.