An yi haduwar ba zata tsakanin Kwankwaso da Ganduje a Sakkwato | Aminiya

An yi haduwar ba zata tsakanin Kwankwaso da Ganduje a Sakkwato

Yadda Ganduje da Kwankwaso suka hadu a Sakkwato
Yadda Ganduje da Kwankwaso suka hadu a Sakkwato
    Ishaq Isma’il Musa

Rahotanni sun bulla cewa an sake yi wata haduwar ba zata tsakanin tsohon gwamnan Jihar Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kuma gwamnan jihar na yanzu, Abdullahi Umar Ganduje a birnin Shehu.

Bayanai sun ce haduwar ta gudana ne ranar Lahadi a filin jirgin sama na Sultan Abubakar III da ke Jihar Sakkwato.

Wasu hotunan haduwar da a yanzu sun baibaye dandalan sada zumunta sun nuna yadda cikin raha aka yi musabaha tsakanin Ganduje da Kwankwaso, duk da cewa akwai tsamin dangartaka ta siyasa da ke tsakaninsu.

Yadda Ganduje da Kwankwaso suka hadu a Sakkwato

Yadda aka hadu tsakanin Ganduje da Kwankwaso

Aminiya ta ruwaito cewa, ko a watan Agustan bara sai da aka yi irin wannan haduwa ta ba zata tsakanin Kwankwaso da Ganduje a filin jirgin saman kasa-da-kasa na Nnamdi Azikwe da ke Abuja, babban birnin kasar.

Waccan haduwa dai an yi ta ne a yayin da jiga-jigan ’yan siyasar biyu ke tsimayen jirgin da zai yi jigilar komawarsu zuwa Kanon Dabo.