✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto

An yi hayagaga tsakanin Amaechi da ejen a zaben fid-da gwanin APC

Hayaniya ta kaure bayan an fara jefa kuri'a a zaben fid-da gwanin jam'iyyar APC

An yi cacar baka tsakanin Ministan Sufuri kuma dan takarar kujerar shugaban kasa a Jam’iyyar APC, Mista Rotimi Amaechi a wurin zaben fid-da gwanin.

Hayagagar ta kaure ne bayan daliget sun fara jefa kuri’a gab da fitowar alfijir na safiyar Laraba a Dandalin Eagles Square da ke Abuja, inda taron yake gudana.

Daga baya dai an samu an shawo kan matsalar sannan aka ci gaba da jefa kuri’a, inda aka umarci wadansu da cikin jamian da ke lura da zaben su sauka daga kan dandali.

An fara zaben ne da daliget din jihar Legas, kuma kawo yanzu, Jihar Anambra ta kammala jefa kuri’a.

Daliget 2,340 ne dai za su yi alkalanci tsakanin mutum 14 da ke neman tikitin takarar shugaban kasa a Jam’iyyar APC mai mulki a zaben 2023.