✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An yi jana’izar tsohon gwamnan Yobe Bukar Abba a Masallacin Harami

An gudanar da jana'izar tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim a Masallacin Harami da ke birnin Makkah a kasar Saudiyya.

An gudanar da jana’izar tsohon Gwamnan Jihar Yobe, Sanata Bukar Abba Ibrahim a Masallacin Harami da ke birnin Makkah a kasar Saudiyya.

A safiyar Litinin, bayan Sallar Subahi aka yi jana’izar tasa tare da wasu mutane kimanin 20.

Sanata Bukar Abba ya rasu ne sakamakon jinya da ya yi fama da ita a Asibitin Saudi-German da ke Saudiyya.

Ya rasu yana da shekaru 75, ya bar mata biyu da ’ya’ya da jikoki.