Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya ce an yi shari’ar ’yan ta’adda 1,000 da ke fuskantar tuhume-tuhume a kotuna daban-daban cikin watanni 18 da suka gabata.
Ministan ya bayyana haka ne a zantawarsa da ’yan jarida a Fadar Shugaban Kasa ranar Alhamis.
- Yajin aikin ASUU masalaha ce ga ’ya’yan talakawa —Sheikh Umar Sani Fagge
- Wike ya musanta kai karar Atiku da Tambuwal kotu
Da yake bayyana ayyukan ma’aikatarsa da irin nasarorin da ta samu ta fuskar gabatar da kara musamman wadanda ake zargi da aikata ta’addanci, Malami ya ce cikin wadannan adadi, 312 na wadanda ta gabatar a gaban alkali, an yanke musu hukunci a tsakanin wadannan watanni.
Cikin wadanda ma’aikatar ta gurfanar, an yanke wa 45 hukunci a kararraki masu sarkakiya a bangaren harkokin teku, da laifukan da suka shafi samar da wutar lantarki na kwamitin kar-ta-kwana.
Malami ya ce ma’aikatar ta gudanar da ayyukan ne tare da hadin gwiwar rassanta 13 da ke fadin kasar, da kuma bangaren da ke kula da shari’ar muggan laifuka na CCG.
Kazalika, ya ce ma’aikatar za ta ci gaba aiki kafada-da-kafada da Babbar Kotu Tarayya da Hukumar Bayar da Taimakon Lauyoyi ta kasa, da kuma Ma’aikatar Tsaro.