✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Sheikh Daurawa da Abba Gida-gida sun sasanta

Wannan dai na zuwa ne bayan da Sheikh Daurawa ya yi murabus a ranar Juma'a.

Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da Shugaban Hukumar Hisbah, Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa, sun yi sulhu a tsakaninsu bayan murabus din malamin daga shugabancin hukumar.

Wannan dai na zuwa ne bayan wata ganawar sirri da malamin ya yi da gwamnan a gidan gwamnatin jihar, a daren ranar Litinin.

Mataimakin Babban Kwamandan Hisbah, Sheikh Mujahid Aminudden, ya ce an yi sulhu tsakanin Sheikh Daurawa da Gwamna Abba ne a karkashin jagorancin Zauren Malaman Kano da ma’aikatan hukumar Hisbah da kuma bangaren jami’an gwamnati.

Daga cikin wadanda suka halarci ganawar akwai, Sheikh Abdulwahab Abdallah, Farfesa Salisu Shehu, Farfesa Borodo, Dokta Sa’idu Dukawa, Dokta Mu’azzam Sulaiman Khalid da sauransu.

Wannan dai na zuwa ne bayan da Sheikh Daurawa ya yi murabus daga shugabancin Hisbah bayan kalaman gwamnan jihar na sukar ayyukan hukumar na kamen masu badala.

Kalaman gwamnan da suka sa Daurawa ya yi murabus sun jawo cece-kuce a jihar.

Murabus din Daurawa ya bar baya da kura, inda mutane suka dinga bayyana ra’ayinsu kan lamarin.

A gefe guda kuwa wasu sun yi ta kira da gwamnan ya bai wa malamin hakuri duba da irin yaki da baɗala da yake yi a jihar.