✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

An Yi Wa Wadume Tarbar Mutunci A Taraba

Sarkin Ibbi ya ce mun godewa Allah da Ya dawo mana da kai lafiya.

Jama’ar Karamar Hukumar Ibbi da ke Jihar Taraba sun fito kan titi domin tarbar mutumin nan da aka zarga da ta’adar garkuwa da mutane da aka ɗaure tun a 2019.

Wata Babbar Kotu a Abuja ce ta yanke wa Hamisu Bala Wadume hukuncin zaman gidan yari na shekara bakwai a gidan kaso na Kuje da ke Abuja a shekarar 2022.

Sai dai a yayin yanke hukuncin, kotun ta ce za a fara lissafin zaman waƙafin da zai tun daga shekarar 2019 lokacin da ya shiga hannu kan laifin da ya aikata.

Kamun Wadume tun a wancan lokacin ya zo da abin mamaki, inda aka zargi sojoji da hallaka wadansu ’yan sanda da ke riƙe da shi kuma suka sake shi ya kama gabansa.

Sai dai daga bisani an sake yin nasarar damke Wadume, inda daga bisani aka miƙa shi kotu har aka yanke masa hukunci.

Wata majiya ta tabbatar mana da cewa an shiga da Wadume Karamar Hukumar Ibbi ne a jirgin ruwa ta Kogin Binuwai.

Musa Garba, wani mazaunin Ibbi ya shaida mana cewa Ibbi ta cika ta batse, an kuma dakatar da dukkanin harkoki a yankin domin tarbar Wadume.

Garba ya ƙara da cewa dandazon mutane ne suka tarbi Wadume, wanda suka haɗa da yara da manya, tsoffi da matasa suka zagaya da shi cikin gari kafin ya isa gidansa.

Wani mai suna Nuhu wanda shi ma mazaunin Ibbi ne ya ce, “muna cikin murna da shagalin biki domin dawowar Wadume daga gida yari.”

Kazalika, Wadume ya kai ziyarar ban girma ga Mai martaba Sarkin Ibbi, Alhaji Salihu Danbawuro inda ya jinjina masa.

A fadar sarki, Wadume ya ce, “na zo ne domin in jinjina maka, in gode maka da mutanen yankin nan, bisa goyon baya da fatan alkhairi da kuka ta yi min tun daga kama ni, zuwa na kotu da kuma zaman gida yari.”

A nasa bangaren, Mai martaba Sarkin Ibbi, Alhaji Salihu Danbawuro ya ce, “Mun gode wa Allah da Ya dawo mana da kai lafiya.”

Wata babbar Kotu a Abuja ce ta tura Wadume gidan yari da ke Kuje, sakamakon tabbatar da laifin tserewa daga hannun jami’an tsaro da kuma mallakar makamai masu nauyi da bai kamata ace wanda ba gwamnati ba yana da irinsu.

Sai dai kotun ta gaza tabbatar da tuhumar da ake yi wa Wadume na satar mutane da neman kuɗin fansa, kamar yadda aka yi zargi a farko.