✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana aiki a boye don a sako Sunday Igboho —Sanwo-Olu

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa akwai mutane da ke aiki karkashin kasa domin ganin an sako dan karajin fafutakar kare yankin Yarbawa,…

Gwamnan Jihar Legas Babajide Sanwo-Olu ya bayyana cewa akwai mutane da ke aiki karkashin kasa domin ganin an sako dan karajin fafutakar kare yankin Yarbawa, Sunday Igboho da ke tsare a birnin Kwatano na kasar jamhuriyar Benin.

Sanwo-Olu ya bayyana haka ne bayan ya kada kuri’a a mazabarsa da ke Ikoyi a zaben kansiloli da shugabanin kananan hukumomi da aka gudanar a jihar a ranar Asabar 24 ga Yuli, 2021.

Bayan ’yan jarida sun tambaye shi game da kan shirun da gwamnonin Jihohin Kudu Maso Yamma suka yi a kan tsare Sunday Igboho, sai gwamnan ya ce akwai mutane da ke aiki a karkashin kasa domin a sako shi.

“Muna cikin mawuyacin hali baki daya, amma mutane na aiki a karkashin kasa, ba tu ne da ba ya bukatar a fito a bayyana,” inji shi.

A ranar Litinin ne jami’an tsaro a birnin Kwatano na kasar Jamhuriyar Benin suka tsare Igboho tare da matarsa a lokacin da suke kokarin ketarewa zuwa Turai daga kasar ta Benin.

Gwamnatin kasar ta gurfanar Sunday Igboho da matar tasa a gaban kuliya a ranar Alhamis inda kotun ta ba da belin matar, shi kuma ta ba da umarnin ci gaba da tsare shi har zuwa lokacin da zai sake gurfana a gabanta a ranar Litinin 26 ga Yuli, 2021.