Ana bikin cika shekaru 20 da kawo karshen yakin basasa a Saliyo | Aminiya

Ana bikin cika shekaru 20 da kawo karshen yakin basasa a Saliyo

Wasu daga cikin yara kanana da ke aikin soji a lokacin yakin basasar shekaru 20 da suka gabata
Wasu daga cikin yara kanana da ke aikin soji a lokacin yakin basasar shekaru 20 da suka gabata
    Ishaq Isma’il Musa

Dubban al’umma a kasar Saliyo sun gudanar da tattaki da bukukuwa a babban birnin Freetown don nuna farin cikinsu na cikar kasar shekaru 20 da kawo karshen yakin basasar da ya tasamma daidaita kasar.

A ranar Talata, 18 ga watan Janairun 2022 ce aka cika shekaru 20 cif da kawo karshen mummunan yakin Basasar da har kawo yanzu radadinsa bai gushe ba a zukatan wadansu da suka kasance ganau kuma jiyau.

An dai kawo karshen yakin basasar Saliyo tun ranar 18 ga watan Janairun 2002 lokacin da tsohon shugaban kasar Ahmed Tejan Kebbah ya sanar da kawo karshen yakin basasar kasar da ya barke a shekarar 1991 a garin Lungi.

Wasu daga cikin yara kanana a aikin soja a lokacin yakin basasar

Yakin dai da ake ganin yana samun goyon bayan wasu kasashen waje, an fara shi ne da nufin kifar da gwamnatin kasar, lamarin da ya yi sanadiyyar mutuwar dubban mutane, da kuma kara yawan yara kanana a aikin soja.

Muryar Amurka ta ruwaito cewa, sama da ’yan gwagwarmaya 70 ne suka taru a garin Lungi don yin maci da nuna farin cikinsu da wanzuwar zaman lafiya a kasar, tun bayan kawo karshen yakin.

’Yan gwagwamaryar dai sun rika wake-waken hadin kan kasa da zaman lafiya da daga tutar kasar da take rainon ingila, kuma guda daga cikin matalautan kasashen na gaba-gaba a duniya, duk da arzikin lu’ulu’un da take da shi.