✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana kama matukan jirgi da mataimakansu 40 sun sha giya kafin tashi sama

Wadanda aka dakatar a watan Afrilu, matuka da ma'aikata ne a wasu kamfanonin jirage biyar

Matukan jirgin sama tara da ma’aikatan cikin jirgi 32 ne aka dakatar bayan an gano sun sha giya gabanin su tuka jirgi a kasar Indiya.

Hukumar Sufurin Jiragen Sama ta Kasar Indiya (DGCA) ta dakatar da su ne bayan gwajin giya da aka yi musu kafin su shiga jirgi ya tabbatar cewa sun kwankwadi barasa.

Ma’aikatan da aka dakatar daga ranar 1 zuwa 30 ga watan Afrilu, sun hada da matukan jirgin kanfanin IndiGo su hudu da mataimakansu 10, sai kuma matukin matukin jirgin kamfanin Go Air da mataimakansa biyar.

Akwai kuma matukin jirgin kamfanin Spice Jet da mataimakansa shida; da matukin jirign India Express da kuma ma’aikatan jirgin Air Asia.

Matukin jirgi daya da ma’aikatan jirgi biyu na kamfanin Vistara, da matukin jirign Alliance Air da kuma ma’aikatan jiring Air India su biyar.

Akwai kuma matukan jirgi bakwai da gwajin ya gano tare da ma’aikatan jirgi 30 da aka gano a karon farko, aka kuma dakatar da su daga aiki na tsawon wata uku.

Kafin barkewar annobar COVID-19, akan yi wa matuka da ma’aikatan cikin jirgi gewajin shan giya kafin su shiga jirgi.

Bayan barkewar annobar aka dakatar da gwajin na dan watanni kafin a sake dawo da yin sh, bayan janye dokokin kariyar cutar.

A watan Afrilu, hukumar DGCA ta dakatar da matukan jirgi 90 na kamfanin Spice Jet daga tuka jirgin Boeing 737 Max bayan ta gano cewa ba su samu horo yadda ya dace ba.

Rahotanni sun nuna cewa hukumar ta kekashe kasa cewa wajibi ne kullum kamfanonin jirage su tabbatar an yi wa akalla rabin ma’aikatansu na cikin jirgi gwajen shan giya.