✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana Neman Fasinjojin Da Suka Faɗa Kogi A Legas

Wadanda abin ya rutsa da su, namiji da mace ne da jami’an ‘yan sandan ruwa ke ci gaba da aikin nemo su a yanzu haka.

Ana ci gaba neman wasu fasinjoji biyu da suka faɗa kogin Legas da ake kira Lagos Lagoon wanda ke karkashin gadar nan ta Third Mainland Bridge.

Hakan ya faru ne biyo bayan hatsarin da ya rutsa da wata motar bas ɗauke da fasinjoji da direbanta ya kauce hanya ya daki makaran gadar.

Wakilinmu ya ruwaito cewa wannan lamari dai shi ya janyo faɗawar fasinjojin biyu cikin kogin a ranar Laraba da ta gabata.

Wani faifan bidiyo da aka yada a kafar intanet  ya nuna lokacin da jami’an ‘yan sandan ruwa ke gudanar da aikin ceto mutanen da suka faɗa kogin.

Haɗarin da ya rutsa da motar kirar bas mai lamba FKJ 872 ya afku ne a yankin Adeniyi Adele na Gadar Third Mainland.

Shugaban hukumar bayar da agajin gaggawa ta kasa mai kula da Kudu maso Yamma, Ibrahim Farinloye ya tabbatar da faruwar lamarin.

A cewarsa, “Direban motar da ke cikin tsala gudu ya kauce daga kan titin, inda ya daki makaran gadar, kuma haka ne ya yi sanadiyar fasinjojin biyu daga cikin motar suka faɗa cikin kogin.”

“Wadanda abin ya rutsa da su, namiji da mace ne da jami’an ‘yan sandan ruwa ke ci gaba da aikin nemo su a yanzu haka.

“An kwashe waɗanda suka jikkata zuwa wani asibiti da ke kusa,” in ji shi.