✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana neman mutane 8 ruwa a jallo kan kisan sojoji a Delta 

A ikin waɗanda aka bayyana ana nema ruwa a jallo akwai wata mata, Igoli Ebi.

Rundunar sojin Najeriya na neman Farfesa Ekpekpo Arthur da wasu mutum shida ruwa a jallo kan zargin alaƙa da kisan dakarunta 17 a Jihar Delta.

A safiyar ranar Alhamis ne dai rundunar sojin kasar ta bayyana sunayen wasu mutane 8 da take nema ruwa a jallo kan kisan sojoji 17 a yankin Okuama na Jihar Delta.

Baya ga Farfesa Ekpekpo Arthur, a cikin waɗanda aka bayyana nema ruwa a jallo akwai wata mata, Igoli Ebi da Ruben Baru da Akata Malawa David da Sinclair Oliki da Clement Ikolo da Andaowei Dennis Bakriri da kuma Akevwru Daniel Omotegbono wanda aka fi sani da Amagbem.

Daraktan yada labarai Hedikwatar Tsaro, Manjo-Janar Edward Buba ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai ranar Alhamis Abuja.

Buba ya yi kira ga masu ruwa da tsaki da masu riƙe da sarautar gargajiya a faɗin kasar nan musamman na yankin Neja-Delta da su taimaka wa sojoji wurin zaƙulo da kama waɗanda ake nema ruwa a jallo.

A baya dai mun kawo muku yadda aka yi wa sojojin runduna ta 181 Amphibious Batallion da ke Karamar Hukumar Bomadi ta Jihar Delta kwanton bauna aka hallaka su akan hanyarsu ta kwantar da tarzoma a ƙauyen Okuoma.

An yi jana’izar jami’an da aka kashe a makabartar sojoji ta kasa da ke Abuja ranar Laraba, inda shugaba Bola Tinubu da wasu manyan jami’an gwamnati suka halarta.