✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana wa yara 980,000 Rigakafin Cututtuka Masu Kisa A Gombe

Kimanin yara 981,710 ’yan kasa da shekara biyar ne ake sa ran yi wa allurar rigakafin shan inna da wasu cututtuka masu kisa a fadin…

Kimanin yara 981,710 ’yan kasa da shekara biyar ne aka fara yi wa allurar rigakafin shan inna da wasu cututtuka masu kisa a fadin Jihar Gombe.

Rigakafin da hukumar kula da lafiya matakin farko ta jihar ta fara gudanarwa ranar Asabar, ana kyautatta tsamanin cimma burin yi wa wadanna yara da aka kiyasta.

Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya ne ya bayyana hakan a lokacin kaddamar da allurar rigakafin a kofar Dagacin Tumfure da ke Karamar Hukumar Akko, a karo na uku.

Gwamna Inuwa wanda ya wakilcin kwamishinan lafiya, Dokta Habu Dahiru, ya ce rigakafin yana daga cikin manufofin shirin Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu na samar wa al’ummar Najeriya kiwon lafiya.

Shi ma mataimakin Shugaban Majalisar Sarakuna na jihar, Mai Kaltungo Injiniya Sale Muhammad, kiran shugabannin al’umma da iyayen yara ya yi musamman mata da cewa su ba da hadin kai wajen ganin an yi wa ’ya’yansu rigakafin, kasancewar allurar ba ta da wata illa kuma za ta kare yaran daga cututtuka masu kisa.

ya da kuma kiyaye Iyaye mata daga mace-mace.

Shi ma wakilin Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) Dokta Ibrahim, cewa ya yi tallafin gwamnatin jihar wajen magance matsalolin kiwon lafiya ya sa ake ganin nan ba da jimawa ba za a kawar da cutar shan inna da sauran cututtukan yara masu kisa.

Dokta Abdurrahaman Shu’aibu Shugaban hukumar kula da lafiya matakin farko a jihar Gombe, ya ce sun kaddamar da allurar rigakafin shan innan ne da tsutsar ciki da cututtukan kananan yara, zazzabin cizon sauro da sauransu, wanda za a dauki tsawon kwanaki hudu daga ranar Asabar 16 zuwa Talata 19 ga watan Disamba 2023.