✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Ana zargin matashi da yi wa yara 8 fyade

’Yan sanda sun gurfanar da wani matashi mai suna Abdurrazak Mohammed Batamele da ke Unguwar Tudun Wadan Pantami, Gombe fadar Jihar Gombe a gaban Kotun…

’Yan sanda sun gurfanar da wani matashi mai suna Abdurrazak Mohammed Batamele da ke Unguwar Tudun Wadan Pantami, Gombe fadar Jihar Gombe a gaban Kotun Majistare ta Biyu da ke Gombe bisa zarginsa da yi wa wadansu kananan yara takwas da suke unguwa daya fyade.

dan sanda mai gabatar da kara Saje Salihu Jibrin, ya ce an kama Abdurrazak Batamele ne a ranar 3 ga Yulin bana, lokacin da ya kira wata yarinya (an sakaya sunanta), mai shekara 3 da suke gida daya ya kai ta dakinsa ya yi mata fyade wanda hakan ya saba wa sashi na 282 na kundin manyan laifuffuka.

Da yake gabatar da Abdurrazak Batamele a gaban kotu Saje Jibrin ya ce an kama shi ne bisa zargin yi wa wadansu yara takwas masu shekara uku da hudu da biyar zuwa 10 fyade a Tudun Wadan Pantami inda ya dauke su daya bayan daya yana kai su dakinsa yana yi musu fyade, kuma aikata hakan ya saba wa sashi na 282 na kundin manyan laifuffuka CPC.

Da kotu ta waiwayi Abdurrazak Batamele, sai ya musanta zargin da ake yi masa, inda dan sanda mai gabagtar da karar ya nemi a dage shari’ar domin ba su dammar kara gudanar da bincke tare da gabatar da shaidunsu. 

Alkalin Kotun Mai shari’a Saluk Idi Yusuf, ya amince da bukatar tare da bayar da umarnin a sakaye wanda ake tuhumar a gidan kurkuku dzuwa ranar 31 ga Agustan nan domin ci gaba da sauraron shari’ar.