Anderlecht na zawarcin dan wasan Najeriya Abdulrazak Ishaq | Aminiya

Anderlecht na zawarcin dan wasan Najeriya Abdulrazak Ishaq

    Abubakar Maccidao

Kungiyar kwallon kafa ta Anderlecht na kasar Belgium tana zawarcin dan wasan Najeriya, Abdulrazak Ishaq daga kungiyar Norrkoping IFK da ke kasar Sweden.

Kungiyar ta Anderletch tana zawarcin dan wasan ne a kan kudi Yuro miliyan 4.5.

Ishaq mai shekara 20 ya fara wasansa ne a kungiyar FC Porto da ke Unguwar Hayin Banki a Karamar Hukumar Kaduna ta Arewa a Jihar Kaduna.

Daga baya ya koma Unity FC Academy da ke Kaduna daga nan kuma ya tsallaka zuwa IFK Norrkoping da ke kasar Sweden.