✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta kori wadanda suka sanar da dakatar da Boss Mustapha daga jam’iyyar

APC ta ce zarge-zargen da aka yi wa Boss din ba su da tushe

Jam’iyyar APC reshen Jihar Adamawa ta kori ’yan kwamitin zartarwarta su 25 saboda rawar da suka taka wajen sanar da dakatar da Sakataren Gwamnatin Tarayya, Boss Mustapha, daga cikinta.

Shugaban jam’iyyar a mazabar da Boss ya fito ne ya sanar da dakatar da shi a makon jiya, bisa zarginsa da yi wa jam’iyyar kafar ungulu a zabukan da suka gabata.

Sai dai mazabar da Sakataren na Gwamnatin Tarayya ya kada kuri’arsa ta Gwadabwa da ke Karamar Hukumar Yola ta Arewa, a makon da ya gabata, ta yi fatali da dakatarwar da kuma zarge-zargen da aka yi masa.

Da yake magana ranar Asabar, a Yola, sakataren jam’iyyar na Jihar, Dokta Raymond Chidama, ya ce an dakatar da mambobin zartaswar da abin ya shafa ne har zuwa wani lokaci daga jam’iyyar.

Ya ce: “Don haka, Kwamitin Ayyuka na Jiha (SWC) ya kalli ayyukan wadannan bata-gari, a matsayin abin kunya ga Shugaban Kasa da Shugaban kasa da kuma daukacin jam’iyya.

“An umarci dukkan ’yan kwamitin da aka dakatar, da su mika kadarorin jam’iyyar ga Shugaban Karamar Hukumar Yola-Arewa cikin gaggawa.”

Ya kuma shawarci dukkan Kananan Hukumomin jam’iyyar da su rika tuntubar masu ruwa da tsaki kafin su yanke hukunci kan kowane mamba.

Daga nan kuma ya ba da umarnin a kafa kwamitin riko na mutum bakwai cikin gaggawa domin karbar ragamar tafiyar da harkokin jam’iyyar a mazabar.