✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta yi babban kamu a Jihar Binuwai

Wasu ‘yan jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Binuwai sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC. Magoya bayan tsohon Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro, Mike Onoja sun…

Wasu ‘yan jam’iyyar PDP mai mulki a Jihar Binuwai sun sauya sheka zuwa jam’iyyar APC.

Magoya bayan tsohon Babban Sakataren Ma’aikatar Tsaro, Mike Onoja sun ce sun koma APC ne saboda PDP mai mulkin jihar ta kasa cika alkawuranta na zaben 2019.

Mutanen da suka ce sun sauya sheka ne domin neman ‘yanci sun ce, “Siyasa hanya ce ta inganta rayuwar galibin jama’a.

“Muna bayyana goyon bayanmu ga APC domin mu hada kai mu ga bayan mulkin PDP a Binuwai ta Kudu da kuma Jihar Binuwai.

“Dukkanninmu mun sha wuyar bakin mulkin PDP kuma muna da rawar takawa wajen gyara kurakuran 2019”, inji Agbo Akorche Simon, babban na hannun daman Onoja.

Da yake jawabi a taron karbar su a Orokam, Karamar Hukumar Ogbadigbo, Agbo ya ce sun sauya sheka ne domin gyara kuskuren da suka yi a zaben 2019.

Ya ce jama’a da su binciki me zai sa a karni na 21 gwamnati ta bar su cikin duhu da rashin tsaftataccen ruwan sha da tabarbarewar hukumomin gwamnati.

Ya ce yanzu za su fara fafutukar ceto jihar da mazaba ta uku gadangadan har sai hakarsu ta cimma ruwa.

A nasa bangaren, shugaban mabiya Onoja a karamar hukumar, Paul Onjefu, ya bayyana gamsuwa da ayyukan Gwamnatin Tarayya karkashin mulkin APC musamman a fannin noma.