✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC ta yi watsi da sabbin manyan kujerun da aka zaba a Majalisun Tarayya

APC ta ce sam ranta bai kwanta da nade-naden ba

Jam’iyyar APC mai mulki ta nesanta kanta daga sabbin jagororin da aka sanar da zaba Majalisar Dattijai da ta Wakilai.

A ranar Talata ce dai Shugaban Majalisar Dattijai, Godswill Akpabio da takawaransa na Majalisar Wakilai, Tajuddeen Abbas, suka sanar da sunayen, yayin zaman majalisun.

Kujerun da aka sanar dai sun hada da Shugabannin Masu Rinjaye da na Marasa Rinjaye da na Mataimakansu da na Masu Tsawatarwa da Mataimakansu a majalisun biyu.

Sanata Akpabio dai ya sanar da Sanata Ali Ndume daga jihar Borno a matsayin mai tsawatarwa na bangaren masu rinjaye da Sanata Rufa’i Hanga daga jihar Kano a matsayin Mataimakin Mai Tsawatarwa bangaren marasa rinjaye.

Sauran jagororin sun hada da Shugaban Masu Rinjaye, Opeyemi Bamidele, Mataimakin Shugaba, David Umahi, da Mataimakin Mai Tsawatarwa ɓangaren masu rinjaye Lola Ashiru.

Daga bangaren maarasa rinjaye kuwa, Sanata Akpabio ya sanar da Simon Davon Mwadkwon a matsayin shugaba, Oyewumi Olalere a matsayin mataimakin shugaba, da Darlington Nwokwocha a matsayin mai tsawatarwa.

A Majalisar Wakilai ma, Abbas ya bayyana Usman Bello Kumo a matsayin mai tsawatarwa bangaren masu rinjaye, sai Aliyu Sani Madakin Gini a matsayin Mataimakin Shugaban Marasa Rinjaye.

Sauran jagororin da shugaban majalisar ya bayyana a bangaren masu rinjaye sun hada da Julius Ihonvbere a matsayin shugaba, Abdullahi Halims mataimakin shugaba, da Adewumi Onanuga mataimakin mai tsawatarwa.

A bangaren marasa rinjaye kuma, Honorabul Abbas ya sanar da Kingsley Chinda a matsayin shugaba, Ali Isa mai tsawatarwa da George Ozodinobi mataimakin mai tsawatarwa.

Amma da yake jawabi ga Gwamnonin jam’iyyar, Shugaban APC na Kasa, Abdullahi Adamu, ya ce ba da yawunsu aka ayyana sabbin jagororin majalisun ba.

Ya ce, “Dazun nan nake jin labari daga wasu kafafen sada zumunta na zamani cewa an yi sanarwa na sabbin kujerun a majalisun tarayya.

“Hedkwatar jam’iyyarmu ta kasa ba ta da kowacce irin masaniya a kan wannan matakin kuma ba a tuntube mu ba.

“A al’adance mu ya kamata mu aika musu a rubuce mu ce ga abin da muka amince da shi. Haka ake yi. Amma duk wata sanarwa da aka yi daga bakin Shugaban Majalisar Dattijai ko mataimakinsa, ko Shugaban Majalisar Wakilai ko Mataimakinsa, babu sa hannun wannan hedkwatar jam’iyyar,” in ji Abdullahi Adamu.