✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

APC za ta kalubalanci nasarar Abba Gida-Gida a kotu

Gawuna ya yi wa Abba Gida-Gida fatan samun nasara a jagoranci.

Jam’iyyar APC reshen Jihar Kano ta shigar da kara a gaban Kotun Sauraron korafe-Korafen Zabe ta jihar tana kalubalantar zaben gwamnan da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.

Mai magana da yawun jam’iyyar, Ahmed Aruwa ne ya sanar da haka ga manema labarai a Kano.

Ahmad Aruwa ya ce jam’iyyar ta shigar da korafinta ne tana karar Hukumar Zabe ta Kasa (INEC) da kuma Jam’iyyar NNPP reshen Jihar Kano.

Jam’iyyar ta APC ta ce sanar da sakamakon zaben da INEC ta yi ya saba da Dokar Zabe duba da cewa an tafka kura-kurai a cikinsa.

Tuni dai jam’iyyar ta shigar da korafin a gaban kotun wanda suka bai wa masana shari’a na jam’iyyar umarnin shigewa a gaba a shari’ar

Aminiya ta ruwaito cewa, dan takarar Gwamnan Kano na APC, Nasiru Yusuf Gawuna ya taya zababben gwamnan jihar, Abba Kabir Yusuf murna bayan da INEC ta ba shi shaidar lashe zabe.