Atiku ya nada Dino Melaye kakakin yakin neman zabensa | Aminiya

Atiku ya nada Dino Melaye kakakin yakin neman zabensa

    Abubakar Muhammad Usman

Dan Takarar Shugaban Kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar, ya nada Sanata Dino Melaye a matsayin kakakin yakin neman zabensa.

A wata sanarwa da mai bai wa Atikun shawara kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ya sanya wa hannu ranar Alhamis, ya bayyana sunan Melaye tare da Dokta Daniel Bwala a matsayin wadanda ya bai wa sabbin mukamai.

“Nade-naden nasu su biyu zai fara aiki nan take,” inji Ibe a cikin sanarwar.

Melaye ya kasance dan majalisar dattawa ta takwas, wanda ya wakilci mazabar Kogi ta Yamma.

Ya fito daga Ayetoro Gbede da ke Karamar Hukumar Ijumu a jihar Kogi.

Bwala, a daya bangaren kuwa, kwararre ne a fannin shari’a, dan siyasa kuma manazarci kan harkokin jama’a.

Ya fito ne daga jihar Adamawa.

Bwala, a baya ya kasance jigo a jam’iyyar APC mai mulki, kafin ya sauya sheka zuwa jam’iyyar PDP saboda takarar Musulmi biyu da APC ta bai wa Bola Ahmed Tinubu da Kashim Shettima.