✕ CLOSE Noma Da Kiwo Hotuna Kiwon Lafiya Girke-Girke Sana'o'i Kimiyya da Kere-Kere Ra'ayin Aminiya Ra’ayoyi Rahoto
Click Here To Listen To Trust Radio Live

Atiku zai yi wa ’yan Najeriya jawabi ranar Litinin — PDP

Atiku zai yi jawabi karon farko bayan hukuncin da Kotun Koli ta yanke kan Zaben 2023.

Dan takarar shugaban kasa karkashin jam’iyyar PDP a zaben 2023, Atiku Abubakar, zai yi wa ’yan Najeriya jawabi da misalin karfe 11:00 na safiyar ranar Litinin.

Aminiya ta ruwaiyo cewa, tsohon Mataimakin Shugaban Kasar zai yi jawabin ne a yayin wani taron manema labarai da zai gudanar a Shekwatar PDP ta kasa da ke Wadata Plaza a Abuja.

Cikin sanarwar da jam’iyyar ta PDP ta wallafa a shafukan sada zumunta ranar Asabar, ta ce Atiku zai yi magana kan wasu muhimman batutuwa da suka shafi kasa.

“Dan takarar shugaban kasa karkashin gagarumar jam’iyyarmu ta PDP a zaben Fabrairu 25 na shekarar 2023 kuma tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, Wazirin Adamawa, zai yi wani muhimmin taro na manema labarai.

“Zai tabo muhimman batutuwa da suka shafi kasa,” a cewar sanarwar wacce ke dauke da sa hannun Sakataren yada labaran jam’iyyar ta PDP.

Wannan zai zamanto karo na farko da Atiku zai yi magana tun bayan da Kotun Koli ta kori karar da ya daukaka yana kalubalantar nasarar Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

A ranar Alhamis Kotun Koli ta kori karar Atiku da ta Peter Obi na Labour Party inda ta jaddada nasarar Tinubu a zaben na 2023.